Home LabaraiGwamnatin Zamfara ta raba buhuna 72,000 na taki ga manoma.

Gwamnatin Zamfara ta raba buhuna 72,000 na taki ga manoma.

12 views

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da shirin rabon kayan tallafin noma na daminar bana, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce na da nufin ƙarfafa samar da abinci da bunƙasa harkar noma.

A yayin ƙaddamar da shirin, gwamnatin jihar ta raba buhuna 72,000 na taki, lita 200,000 na magungunan kashe ciyawa, tare da injuna 100 na sarrafa ragowar amfanin gona domin amfanin manoma a faɗin jihar.

Haka kuma, gwamnatin ta raba injuna 100 na yankan ciyawa, injuna 100 na niƙa abincin dabbobi, da kuma iri na ingantacciyar ciyawar kiwo. Bugu da ƙari, an bai wa jami’an wayar da kan manoma babura 20 da wayoyin hannu 20 domin sauƙaƙa musu gudanar da ayyukansu.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da Allah Ya albarkaci ƙasa mai kyau da ta dace da noma a Najeriya. Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen farfaɗo da harkar noma domin ƙara yawan samar da abinci, samar da ayyukan yi ga matasa, rage talauci da kuma inganta tattalin arzikin jihar.

Ya kuma buƙaci manoman da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin cimma burin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci a jihar da ƙasa baki ɗaya.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 0   +   9   =