Home LabaraiGwamnatin Sokoto Za Ta Tallafa Wa Sabbin Likitoci Da Guraben Koyon Aiki.

Gwamnatin Sokoto Za Ta Tallafa Wa Sabbin Likitoci Da Guraben Koyon Aiki.

17 views

Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi alkawarin taimaka wa likitocin da suka kammala karatunsu a ƙasashen waje, tare da samar musu da guraben koyon aikin likitanci a asibitocin jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar likitocin a ma’aikatar lafiya.

Ya kuma umurci hukumomin lafiya da su fara shirye-shiryen samar musu da guraben koyon aiki, domin su ƙara ƙwarewa tare da bayar da gudummawa ga inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

Kwamishinan ya buƙaci likitocin da su nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen yi wa al’ummar jihar hidima, bisa la’akari da jarin da gwamnati ta zuba wajen karatunsu.

A nasa jawabin, shugaban tawagar likitocin, Dakta Abdulnasir Bashiru Sulaiman, ya gode wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa tallafin da suka samu, tare da neman ci gaba da goyon bayan gwamnati domin kammala sauran matakan ƙwarewarsu.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 8   +   10   =