Home SiyasaPDP Ta Fara Tattaunawa da INEC Kan Cire Sunayen Wasu ’Yan Takararta

PDP Ta Fara Tattaunawa da INEC Kan Cire Sunayen Wasu ’Yan Takararta

13 views

moonJam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara tattaunawa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin warware matsalar cire sunayen wasu daga cikin ’yan takararta a jerin sunayen ƙarshe da hukumar ta fitar.

 

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Hon. Jungudo Haruna Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar na ɗaukar lamarin da muhimmanci, kuma tana ƙoƙarin ganin an warware matsalar bisa tanade-tanaden dokokin zaɓe da ƙa’idojin hukumar INEC.

 

Ya ce PDP za ta ci gaba da sanar da jama’a halin da ake ciki yayin da tattaunawar da hukumar zaɓen ke gudana. Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta himmatu wajen tabbatar da cewa an magance dukkan korafe-korafen da suka dace.

 

Haka kuma, jam’iyyar ta buƙaci ’yan takarar da abin ya shafa, mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu, tare da guje wa duk wani mataki ko furuci da zai iya kawo cikas ga tattaunawar da take yi da INEC.

 

 

 

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   10   =