Home LabaraiSokoto: An gudanar da addu’o’i na musamman ga Najeriya a ranar ’Yancin Kai.

Sokoto: An gudanar da addu’o’i na musamman ga Najeriya a ranar ’Yancin Kai.

25 views

Gwamnatin Jihar Sokoto ta gudanar da addu’o’i na musamman a masallatan Juma’a takwas da ke cikin birnin Sokoto, domin neman rahama, shiriya da kariyar Allah ga Najeriya, yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Addu’o’in sun mayar da hankali kan matsalolin tsaro, zaman lafiya da kuma neman taimakon Allah ga shugabannin ƙasar wajen shawo kan ƙalubalen da ke addabar Najeriya.

Malaman sun kuma yi addu’ar samun nasara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu a zaɓukan da ke tafe, tare da roƙon Allah Ya ba da damar gudanar da zaɓen 2027 cikin zaman lafiya.

An gudanar da addu’o’in ne tare da halartar manyan jami’an gwamnatin jihar da shugabannin jam’iyyar APC da sauran jami’an tsaro.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 4   +   6   =