Gwamnatin Jihar Sokoto, ta hannun Mataimakin Gwamna, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ta yi kira da a inganta tattara bayanan sirri, samar da isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan tsaro da kuma ƙarfafa ɗaukar alhakin ayyuka domin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Alhaji Idris Gobir ya yi wannan kiran ne a Abuja, yayin da yake wakiltar Gwamna Ahmed Aliyu a wani taron tattaunawa kan hanyoyin magance ta’addanci, wanda Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Rikice-rikice ta Bonn (BICC) da sauran abokan hulɗa. Ya nuna damuwa kan ayyukan ’yan bindiga a yankunan da ke iyaka da jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi, tare da buƙatar ƙara sa ido da amfani da bayanan sirri daga al’ummomi domin gano maboyar masu aikata laifuka.
A nasa jawabin, Mai Gudanarwa na Ƙasa na NCTC, Janar Adamu Garba Laka, ya jaddada cewa yaƙi da rashin tsaro na buƙatar haɗa ayyukan soji da ingantaccen shugabanci, hulɗa da al’umma da shirye-shiryen gyara rayuwar waɗanda suka fice daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai. Shi ma Mataimakin Jakadan Jamus a Najeriya ya bayyana cewa ƙasar ta bayar da tallafin sama da Yuro miliyan 80 ga shirin Northwest Prevention Facility domin tallafa wa ayyukan samar da zaman lafiya da inganta rayuwar al’umma.
A ƙarshe, wakiliyar Hukumar Tarayyar Afirka, Mrs Joselyns Nehimana, da babban mai bincike a cibiyar BICC, Dakta Oyawale Ohimini, sun jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashe da kuma magance hanyoyin kuɗi da yaɗa bayanan ƙarya da ke taimaka wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka. An gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu ne domin tattauna hanyoyin dakile tashe-tashen hankula da han
a ɗaukar sabbin mambobi cikin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.