Home LabaraiMTN: Dakatar da rancen katin waya da data na wucin gadi ne

MTN: Dakatar da rancen katin waya da data na wucin gadi ne

57 views

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sanar da dakatar da tsarin rancen katin kiran waya da na data da ake kira Xtratime na wucin gadi.

Kamfanin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin bin sabbin ƙa’idojin da Hukumar Kare Gasa da Kare Masu Amfani (FCCPC) ta fitar a shekarar 2025.

A cikin wata sanarwa da sakataren kamfanin, Uto Ukpanah, ya aike wa kamfanin hada-hadar hannun jari na Najeriya (NGX), MTN ya ce dakatarwar ta shafi tsarin rancen kiran waya da data gaba ɗaya.

Tsarin Xtratime dai yana bai wa kwastomomin da ke kan tsarin prepaid damar aron katin kiran waya ko data, wanda za su biya daga baya bayan sun sake saye.

Kamfanin ya ce wannan tsari ya fada karkashin sabbin dokokin da ke bukatar masu bayar da rancen dijital su samu lasisi na musamman tare da bin ƙa’idoji na doka.

Haka kuma, MTN ya jaddada cewa dakatarwar na wucin gadi ce, kuma an dauke ta ne domin daidaita ayyukansa da sabbin dokokin da aka kafa.

Duk da wannan mataki, kamfanin ya tabbatar wa kwastomominsa cewa za su ci gaba da samun damar siyan katin waya da data ta hanyoyin da aka saba, yana mai cewa dakatarwar ba za ta yi tasiri sosai ga ribar kamfanin ba.

Sabbin ƙa’idojin FCCPC na shekarar 2025 sun fadada ikon kula da rancen dijital, inda suka shafi kamfanonin sadarwa da sauran masu bayar da rance na gajeren lokaci.

Ƙa’idojin sun tanadi cewa dole ne duk masu irin wannan harkar su yi rajista tare da samun amincewa kafin su ci gaba da aiki, inda aka sanya wa’adin cika wannan sharadi kafin watan Afrilun 2026.

Masana sun ce tsaurara waɗannan ƙa’idoji na da nasaba da damuwa kan karuwar basussuka, tsaron bayanan kwastomomi, da kuma yadda ake tafiyar da harkokin rancen dijital a Najeriya.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 4   +   4   =