Home LabaraiBa sulhu da ‘yan bindiga sai sun mika wuya – Gwamna Aliyu

Ba sulhu da ‘yan bindiga sai sun mika wuya – Gwamna Aliyu

112 views

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun cimma matsaya cewa ba za su shiga wata tattaunawa da ‘yan bindiga ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Jihar Katsina yayin kaddamar da titin Yandaki–Shinkafi–Kofar Sauri mai tsawon kilomita 8.1 da aka gina kan kudi naira biliyan 12.6, wanda Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya aiwatar.

Aliyu ya ce gwamnonin yankin sun hada kai wajen kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin, inda ya kara da cewa gwamnatocin jihohi na kashe kudade masu yawa domin magance matsalar.

Ya jaddada cewa ba za su karbi wata tayi daga ‘yan bindiga ba face sun mika wuya ba tare da sharadi ba.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnatoci na aiki tare da hukumomin tsaro domin inganta dabarun kawo karshen ‘yan bindiga da sauran laifuka.

Ya bukaci al’umma da su ba da hadin kai ga gwamnati da jami’an tsaro ta hanyar fallasa masu bai wa ‘yan bindiga bayanai a cikin al’umma, yana mai cewa babu wani hari da ke faruwa ba tare da taimakon wasu daga cikin jama’a ba.

Haka kuma ya shawarci jama’a da su kasance masu lura da motsin mutane da ba su sani ba a yankunansu.

Gwamna Aliyu ya yabawa Gwamnan Katsina kan kafa rundunar ‘Community Guard’, yana mai cewa wannan tsari zai taimaka wajen karfafa yaki da ‘yan bindiga.

Ya kuma bayyana cewa bayan ya halarci kaddamar da rundunar a Katsina, shi ma ya koma Sakkwato ya kafa irin wannan runduna.

A karshe, ya yabawa Gwamna Dikko Umaru Radda, shugaban dandalin gwamnonin APC na Arewa maso Yamma, bisa jagoranci mai inganci.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 3   +   5   =