Home LabaraiZaɓi biyu da suka rage wa PDP gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027

Zaɓi biyu da suka rage wa PDP gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027

PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin mafi daɗewa. Jam'iyyar ce ta mulki Najeriya daga 1999 lokacin da ƙasar ta koma mulkin dimokuraɗiyya har zuwa shekara ta 2015, sai dai rikicin da ke addabar jam'iyyar ta sa ta yi asarar jihohi 31 ga jam'iyyar APC mai mulki.

79 views

PDP ita ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin mafi daɗewa. Jam’iyyar ce ta mulki Najeriya daga 1999 lokacin da ƙasar ta koma mulkin dimokuraɗiyya har zuwa shekara ta 2015, sai dai rikicin da ke addabar jam’iyyar ta sa ta yi asarar jihohi 31 ga jam’iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar da ya kamata ta zamo barazana, a yanzu tana cikin mawuyacin hali inda ta dare zuwa ɓangarori, hakan ya sanya tana cikin barazana gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

Yayin da ake faman kai-komo a kotu, yanzu jam’iyyar ta dare zuwa gida biyu, ɗayan ɓangaren na ƙarƙashin gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da na Bauchi Bala Mohammed.

Ɗayan ɓangaren kuma na yin biyayya ga ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, wanda ya ƙi fita daga jam’iyyar duk da cewa yana riƙe da muƙami a gwamnatin Bola Tinubu ta jam’iyyar APC.

Yanzu akwai kimanin ƙararraki 9 a gaban kotu game da halin da PDP ke ciki. Lamarin ya sanya gwamnonin jam’iyyar da dama suka fice daga cikinta.

A baya-bayan nan ne kotun ɗaukaka ƙara ta sake tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu kan cewa kada hukumar zaɓen Najeriya ta amince da zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka yi a garin Ibadan na jihar Oyo a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025.

A taron na garin Ibadan ne ƴaƴan jam’iyyar suka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa da kuma Taofeek Arapaja a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa, da kuma sauran shugabanni.

A lokacin taron ne jam’iyyar ta kori ministan Abuja Nyesom Wike, da Ayo Fayose da wasu manyan jam’iyyar bisa zargin su da ayyukan zagon-ƙasa.

Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun buƙaci ɓangaren Tanimu Turaki ya amshi hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na baya-bayan nan, tare da sulhuntawa da ɓarin Nyesom Wike, ta yadda jam’iyyar za ta sake yin wani babban taro, kasancewar wasu na tsoron cewa hukumar zaɓen Najeriya ta INEC na iya haramta mata fitar da ƴan takara a zaɓen 2027 idan rikicin ya ci gaba.

Yayin da jam’iyyar ke fama da wannan rikice-rikice, jadawalin hukumar zaɓe ya nuna cewa jam’iyyu za su yi zaɓen fitar da gwani ne tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayun wannan shekara ta 2026.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 2   +   5   =