Home LabaraiJihar zamfara ta ware Naira biliyan 6.271 domin bunƙasa noma.

Jihar zamfara ta ware Naira biliyan 6.271 domin bunƙasa noma.

3 views

Majalisar Zartaswa ta Jihar Zamfara ta amince da kashe Naira biliyan 6.271 domin aiwatar da Shirin Ƙasa na Inganta Noma ta Hanyar Amfani da Injina na “Renewed Hope” na Gwamnatin Tarayya.

An cimma wannan matsaya ne a taro na 13 na Majalisar Zartaswa, bayan Kwamishinan Noma ya gabatar da takardar neman amincewa da shirin.

A ƙarƙashin shirin, gwamnatin jihar za ta sayo taraktoci 100 da sauran kayan aikin noma, tare da kafa Cibiyar Ayyukan Injinan Noma (Agri-Hub) a Gusau domin inganta ayyukan noma da sauƙaƙa wa manoma samun injinan noma.

Majalisar ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage kuɗin noma, ƙara yawan amfanin gona, samar da wadatar abinci da kuma samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar jihar.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta na ci gaba da zuba jari a fannin noma domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 4   +   2   =