Home LabaraiGwamnatin Kaduna na ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsarin sufuri na zamani

Gwamnatin Kaduna na ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsarin sufuri na zamani

187 views

Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar abokan hulɗarta sun ƙara ƙaimi wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aiwatar da shirin Kaduna Bus Rapid Transit (KBRT), wani tsari da ake sa ran zai kawo sauyi a harkar sufuri a Arewacin Najeriya.

A yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar 8 ga Afrilu, 2026 a KADSTRA Kaduna, da kuma ganawa da sarakunan gargajiya a ranar 16 ga Afrilu, jami’an aikin sun yi bayani kan yadda aikin ke tafiya da kuma tsarin da aka tsara na aiwatar da shi. Shirin, wanda aka fi sani da Kaduna Connect, na da nufin rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirgar jama’a.

Da yake jawabi, Darakta Janar na KADSTRA, Injiniya Inuwa Ibrahim, ya bayyana cewa shirin shi ne irinsa na farko a Arewacin Najeriya, yana mai cewa zai taimaka wajen inganta tsaro, sauƙaƙa sufuri da bunƙasa tattalin arziki.

Shi ma Daraktan aikin, Injiniya Yamusa Bello Yamusa, ya ce wannan shiri wani babban mataki ne na tarihi ga jihar Kaduna da ma ƙasar baki ɗaya, tare da jaddada muhimmancin haɗa dukkan masu ruwa da tsaki, musamman sarakunan gargajiya.

A nasa ɓangaren, Mai kula da aikin, Injiniya Usman Aliyu, ya ce an tsara KBRT ne domin samar da ingantaccen tsarin sufuri na zamani da zai taimaka wajen ci gaban birane da tattalin arziki.

Haka kuma, Shugaban ƙungiyar tsara aikin (PMOD), Ted Regino, ya jaddada muhimmancin rawar da masu ruwa da tsaki ke takawa wajen nasarar shirin, yayin da ƙwararren masani kan al’umma, Dakta Abdulkadir Jafar, ya tabbatar da ci gaba da sauraron ra’ayoyin jama’a domin inganta aikin.

Rahotanni sun nuna cewa shirin zai ƙunshi kusan tashoshin mota 30 da manyan motocin bas masu ɗaukar fasinjoji da yawa, waɗanda za su yi aiki a kan hanyoyi 10 a matakai daban-daban. Hanyar farko za ta fara daga Gonin Gora zuwa Rigachikun, ta ratsa wurare da suka haɗa da Refinery Junction.

A bangaren gina hanyoyi kuwa, za a shimfiɗa kusan kilomita 24 daga gadar Kawo zuwa NNPC Junction, tare da amfani da sabbin fasahohi kamar hanyoyin bas na musamman, tashoshi na zamani, kariyar masu tafiya a ƙafa, da tsarin biyan kuɗi na lantarki.

Masu ruwa da tsaki sun nuna goyon baya ga shirin, tare da yaba yadda aka yi la’akari da muhimman batutuwa kamar tsaro, muhalli da haɗa tsarin sufuri da ake da shi.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada aniyar ta na tabbatar da gaskiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa wajen aiwatar da shirin KBRT.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 3   +   4   =