Home LabaraiDr. Fatima Zuntu ta karɓi jagorancin NBMA

Dr. Fatima Zuntu ta karɓi jagorancin NBMA

604 views

 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Dr. Fatima Suleiman Zuntu a matsayin sabuwar Darakta Janar/ Shugaba na Hukumar Kula da Tsaron Halittu ta Ƙasa (NBMA).

 

A cewar sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, naɗin nata zai fara aiki ne daga ranar 16 ga Afrilu, 2026, na wa’adin shekaru huɗu na farko, bisa tanadin dokar hukumar ta 2015.

 

Dr. Fatima Zuntu ƙwararriya ce a fannin kiwon lafiya da tsara manufofi, kuma ta taka muhimmiyar rawa a shirye-shiryen gwamnati daban-daban na ƙasa.

 

Shugaba Tinubu ya buƙaci sabuwar shugabar da ta yi amfani da ƙwarewarta wajen inganta ayyukan hukumar domin ci gaban ƙasa.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 7   +   3   =