Home LabaraiNijeriya na neman Turkiyya ta sasanta ta da Nijar domin ƙarfafa tsaro

Nijeriya na neman Turkiyya ta sasanta ta da Nijar domin ƙarfafa tsaro

290 views

Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa ƙasar na neman taimakon Turkiyya domin shiga tsakani wajen gyara alaƙarta da Jamhuriyar Nijar, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a yankin Tafkin Chadi.

 

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da TRT Afrika Hausa a Taron Diflomasiyya na Antalya, inda ya ce sun roƙi Turkiyya ta yi amfani da alaƙarta da Nijar don ƙarfafa ta komawa cikin haɗin gwiwar tsaro na yankin.

 

Ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai, yana mai cewa ‘yan ta’adda ba sa girmama iyakoki, don haka haɗin kai tsakanin ƙasashe yana da matuƙar muhimmanci.

 

Musa ya ƙara da cewa haɗin gwiwar ƙasashen yankin kamar Chadi da Kamaru na taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, tare da nuna fatan Mali da Burkina Faso za su ci gaba da aiki tare da Nijeriya.

 

Dangane da haɗin gwiwa da Amurka, ministan ya ce a halin yanzu ana mai da hankali ne kan horo da tsara dabaru, yana mai cewa irin wannan aiki na buƙatar lokaci kafin a fara ganin sakamako.

 

Ya kuma tabbatar da cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiki da ƙasashen da ke da niyyar taimakawa wajen samar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala a gaba ba.

You may also like

Leave a Comment

Prove your humanity: 8   +   8   =